1. What is a Multimeter? / Mene ne Multimeter?
English: A multimeter is an electronic tool used to measure voltage, current, and resistance. In smartphone repair, it is our "eyes" because it helps us see what is happening inside the motherboard where our eyes cannot reach
Hausa: Multimeter wata na'ura ce da ake amfani da ita wajen auna ƙarfin wuta (voltage), kwararar wuta (current), da kuma duba cikas (resistance). A gyaran waya, ita ce "idonmu" domin tana taimaka mana mu ga abin da yake faruwa a cikin motherboard inda idonmu ba zai iya gani ba
2. Important Parts / Muhimman Sassan Multimeter
English: * Display: Shows the measurement numbers
Dial/Knob: Used to select the function (Voltage, Continuity, etc.)Probes: The Red probe is Positive (+), and the Black probe is Negative (-)
Hausa: * Display (Fuska): Inda lambobin sakamakon gwajin suke fitowa
Knob (Maballin Juya-juya): Inda kake zaɓar abin da kake son aunawa.
Probes (Wayoyi): Jan waya ita ce Positive (+), Bakar waya kuma ita ce Negative (-)
3. How to Use it for Repairs / Yadda ake amfani da ita wajen Gyara
A. Checking Battery & Charger (DC Voltage)English: Set the dial to DCV 20V. Use this to check if a battery is charged or if a charging port is bringing out 5V
Hausa: Saita maballin zuwa DCV 20V. Yi amfani da wannan wajen duba ko batir yana da caji, ko kuma ko chaja tana fitar da wuta (5V)
B. Finding Short Circuits (Continuity Mode)
English: Set the dial to the Beep/Wi-Fi icon. If the multimeter makes a sound (beep) when touching a component, it means there is a direct connection or a short circuit
Hausa: Saita maballin zuwa inda akwai alamar sauti (Beep). Idan multimeter ta yi kuka (beep) yayin da ka taɓa wani yanki, hakan na nufin akwai "short circuit"C. Diode Mode (Testing Lines)
English: Used to compare readings on a good board vs. a bad board to find broken lines
Hausa: Ana amfani da shi wajen duba lafiyar layukan wuta na motherboard ta hanyar kwatanta lambobin dake fitowa
4. Conclusion / Kammalawa
English: You cannot be a professional smartphone engineer without knowing how to use a multimeter. It is the most important tool at Pro Device Fix
Hausa: Ba za ka zama kwararren injiniyan gyaran waya ba har sai ka san yadda ake amfani da multimeter. Ita ce mafi mahimmancin kayan aiki a shagon Pro Device Fix



0 Comments